Home Labaru Takaddama: ‘Yan Nijeriya Na Caccakar Femi Fani-Kayode A Kan Komawa APC

Takaddama: ‘Yan Nijeriya Na Caccakar Femi Fani-Kayode A Kan Komawa APC

15
0
Femi

Mamaki ya cika ‘yan Nijeriya da dama, bayan samun labarin sauya sheƙar da Femi Fani-Kayode ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa ta APC.

Fani-Kayode, wanda ake yi wa kallon ya fi kowa adawa da gwamnatin Shugaba Buhari, sai ga shi a karshe ya koma inuwa guda da abokin gabar sa.

Kalaman Fani-Kayode a baya dai sun rika faranta wa masu adawa da jam’iyyar APC zukata, tare da muzanta wa gwamnati da muƙarraban ta.

Tuni dai ‘yan Nijeriya na cigaba da bayyana ra’ayoyin su, musamman a shafukan sada zumunta game da wanna lamari mai cike da al’ajabi.

Wani abu da ya fi ba ‘yan Nijeriya mamaki har ya sa su ke caccakar Fani-Kayode shi ne, inda ya ce dalilin sa na komawa APC saboda shugaba Buhari ya sauya ne, lamarin da ke nufin ba Buharin da ya riƙa su  ka ba ne a baya.