Majalisar dattawa ta bayyana shirin ware wa ‘yan sanda kasafin kudi na musamman don ganin sun gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.
Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan ya bayyana haka, yayin da shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu da tawagar sa su ka kai masa siyara ofishin sa da ke Abuja.
Shugabannin biyu dai sun tattauna batun wata doka da ta shafi makarantar horar da ‘yan sanda da kuma asusun musamman ga rundunar ta kasa.
A karshe Shugaban majalisar dattawan ya ce, akwai bukatar a sake tsarin gudanar da ayyukan rundunar ‘yan sanda, domin tabbatar da ganin sun samu horon da ya dace da kuma ba su kula ta musamman.
You must log in to post a comment.