Home Labaru Kudin Shiga: Majalisar Dattawa Ta Bayyana Burin Ta A Kan Sabis Na...

Kudin Shiga: Majalisar Dattawa Ta Bayyana Burin Ta A Kan Sabis Na 5G

13
0

Majalisar Dattawa ta bukaci Hukumar Sadarwa ta kasa ta yi amfani da tsarin sadarwa na 5G domin sama wa Gwamnatin Tarayya kudin shiga Naira Biliyan 350 a cikin kasafin shekara ta 2022.


Idan dai ba a manta ba, gwamnatin tarayya ta amince a fara amfani tsarin sadarwa na 5G a Nijeriya.
Shugaban kwamitocin hadin gwiwa na majalisun dokoki Sanata Solomon Adeola, ya ce kasafin Hukumar Sadarwa na shekara ta kudin 2022 ba zai kasanceNaira Biliyan 115 ba kamar yadda ta yi hasashe.
Yayin da Shugaban Hukumar NCC Umar Danbatta ya ke kare kasafin hukumar a gaban kwamitin Majalisar Dattawa, ya ce hukumar za ta iya samar da Naira biliyan 400 daga tsarin sadarwa na 5G.