Home Labaru Ilimi Illar Ta’addanci: Gwamnantin Tarayya Ta Fara Sake Gina Makarantu A Yobe

Illar Ta’addanci: Gwamnantin Tarayya Ta Fara Sake Gina Makarantu A Yobe

32
0

Gwamnatin Tarayya, ta fara aikin sake gina makarantun da mayakan Boko Haram su ka ragargaza a Jihar Yobe da sauran sassan jihohin Arewa maso Gabas.

Shirin dai, an fara shi ne a ƙarƙashin Hukumar Bunƙasa Yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya NEDC, wadda ke ƙarƙashin Ma’aikatar Agaji da Jinƙai da Inganta Rayuwa ta Ƙasa.

Gwamnatin Jihar Yobe ta bada filaye domin gina makarantu a Potsdam da Buni Yadi da Gashua cikin Ƙaramar Hukumar Bade.

Shugaban Hukumar Mohammed Alƙali ya bayyana haka a Gasua, inda ya ce an bijiro da shirin ne don a gaggauta shawo kan ƙarancin makarantu da azuzuwan karatu.

Ya ce matsalar ƙarancin azuzuwan makarantun sakandare da na Firamare duk ayyukan ta’addancin Boko Haram ne su ka haddasa shi, sun kuma maida yankin Arewa maso Gabas wanda ya fi fama da fatara da talauci a Nijeriya, kuma shi ne koma-baya wajen taɓarɓarewar ilmi.