Home Labaru Kudin Shiga: Hukumar Tara Haraji Ta Tara Naira Tiriliyan 1.5 Cikin Wata...

Kudin Shiga: Hukumar Tara Haraji Ta Tara Naira Tiriliyan 1.5 Cikin Wata Uku

335
0
Babatunde Fowler, Shugaban Hukumar Tara Kudaden Haraji Na Najeriya, FIRS

Hukumar tara kudaden haraji na Najeriya FIRS, ta ce ta tara kudi Naira tiriliyan 1 da rabi a watanni ukun farkon shekarar 2019.

Shugaban hukumar Babatunde Fowler, ya bayyana haka ga wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a birnin New York, na kasar Amurka.

Ya ce kudaden harajin sun hada da harajin kudaden shiga da ba na bangaren harkokin man fetur da gas ba, wadanda ya ce sun haura wanda aka samu a watanni ukun farko na shekarar 2018 da kaso 11 bisa 100.

Babatunde Fowler, ya je New York ne domin taron da Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyi a kan hanyoyin da za a toshe kafafe da kofofin da ake hada-hada da haramtatttun kudaden sata, ko wadanda ake samu ta hanyar manyan laifuka irin cinikin haramtattun kwayoyi da makamai.

Ya ce an samu fiye da Naira tiriliyan 1 a watanni uku na farkon 2018, yanzu kuma an samu Naira tiriliyan 1 da rabi, wato an samu kari na Naira bilyan 330 kenan.Hukumar FIRS dai tun farkon shekarar nan ta ce ta na sa ran tara kudaden shiga har naira tiriliyan 8 a cikin shekarar 2019.

Leave a Reply