Gbong Gwom Jos, kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Filato, Jacob Buba Gyang, ya ce Gwamnan Jihar Simon Lalong, ba shi da ikon rarraba masarautun jihar.
Basaraken ya yi wannan furuci ne a Jos, babban birnin Jihar Filato a wajen wani taro na gangamin bikin Al’adun Kabilar Birom na bana.
Ya ce yana wannan kalamin ne a matsayin martani dangane da wata sanarwa da gwamnatin Jihar ta bayar, na kirkiro wasu sabbin masarautu biyu a Jihar.
A halin da ake ciki dai idan aka kirkiro masarautun Jos ta Arewa da Birom, zai rage wa Gbong Gwom karfi da yawan masarauta domin za’a barshi da kananan hukumomi biyu ne rak, su ne Jos ta Kudu da Barkin Ladi.Sanarwar da aka fitar ta nuna cewa basarake Attah na Ganawuri zai zama Sarkin Birom, inda shi kuma Sarkin Anaguta da Afizere zai kasance rike da mukaman sarauta biyu a Jos ta Arewa.