Home Labaru Kudin Haraji: Gwamnatin Kaduna Ta Garkame Ofisoshin Bankin Access Uku

Kudin Haraji: Gwamnatin Kaduna Ta Garkame Ofisoshin Bankin Access Uku

355
0

Hukumar Karbar Harajin dole ta jihar Kaduna, ta garkame Ofisoshin bankin Access uku da ke cikin garin Kaduna, wadanda su ka hada da bankin da ke Titunan Ahmadu Bello da Isa Kaita da kuma wanda ya ke kan titin Bida.

Lauyan hukumar Francis Kozah, ya ce tun a shekarun baya ne su ka sanar da bankin cewa jihar Kaduna na bin su kudin haraji har naira miliyan 175.

Ya ce amma duk da kokarin da su ka yin a samun matsaya game da yadda za a biya harajin haka ba ta cimma ruwa ba, don hukumar ta dauki matakin rufe wasu daga cikin ofisoshin bankin har sai sun biya kudadaden da ake bin su, kuma ko da sun biya sai sun biya kudin wahalar kulle harabar bankunan da gwamnati ta yi.

Shugaban hukumar Zaid Abubakar, ya ce gwanatin jihar Kaduna ba za ta daga wa kowa kafa ba, ya na mai cewa duk wani mai sana’a ko mai kamfani da manyan ofisoshi a jihar, ya tabbatar ya biya bashin aharajin da ake bin shi ko kuma ya kuka da kan sa.