Home Labaru Za Mu Shiga Yajin Aikin Gama-Gari Ranar 16 Ga Watan Oktoba –...

Za Mu Shiga Yajin Aikin Gama-Gari Ranar 16 Ga Watan Oktoba – TUC

374
0
Za Mu Shiga Yajin Aikin Gama-Gari Ranar 16 Ga Watan Oktoba - TUC
Za Mu Shiga Yajin Aikin Gama-Gari Ranar 16 Ga Watan Oktoba - TUC

Gamayyar Kungiyoyin Kwadago ta Nijeriya, ta yi Barazanar shiga yajin aikin gama-gari matukar hukumomin Nijeriya ba su fara aiwatar da tsarin biyan mafi karancin albashin ma’aikata ba.

Haka kuma, Kungiyar ta sha alwashin kassara harkokin Nijeriya baki daya a ranar 16 ga watannan Oktoba, idan har ba a fara biyan sabon albashin ba.

A baya dai hukumomi da kungiyoyin kwadago sun cimma matsaya kan lamarin, amma bayanai na nuni da cewa, har yanzu ba a fara aiwatar da sabon tsarin ba.

Mukaddashin Babban Sakataren kungiyar Comrade Nuhu Toro, ya ce yajin da za su shiga a ranar 16 ga watan Oktoba na gama-gari ne, don haka za su tabbatar da ganin duk ma’aikatan Nijeriya ba su fito aiki ba.

Nuhu Toro ya kara da cewa, za su durkusar da filayen jiragen sama, sannan hatta wautar lantarki ba za a same ta ba a duk fadin Nijeriya.