Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce za ta dauki ma’aikatan wucin-gadi dubu 16 da 139, domin gudanar aikin zaben gwamnan jihar Kogi da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.
Kakakin hukumar zabe ta kasa Festus Okoye ya bayyana haka, yayin wani shirin sanin makamar aiki da horarwa da aka gudanar a kwalejin gwamnatin tarayya da ke Okene.
Ya ce hukumar zabe na bukatar wannan adadi na ma’aikata, domin zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a rumfunan zabe dubu 2 da 548 a cikin unguwanni 239 na jihar.
Festus Okoye ya kara da cewa, yayin da ake daf da kammala duk wani shiri, nan da mako biyu duk kayayyakin zaben za su kasance a jihar.