Home Ilimi Ku Ɗaina Tura ‘Ya’Yan Ku Karatu Arewacin Cyprus – Gwamnatin Nijeriya

Ku Ɗaina Tura ‘Ya’Yan Ku Karatu Arewacin Cyprus – Gwamnatin Nijeriya

451
0

Ma’aikatar kula da harkokin ‘yan Nijeriya mazauna ketare, ta gargadi iyaye su daina tura ‘ya’yan su yankin Arewacin Kasar Cyprus saboda tsananin rashin tsaro da ke yankin.

Shugabar ma’aikatar Abike Dabiri-Erewa ta sanar da haka, a wani taro da ma’aikatar ta yi da manema labarai a makon da ya gabata, inda ta ce an kashe dalibai ‘yan Nijeriya a Arewacin
kasar Cyprus da dama, saboda yankin har yanzu ba kasa bace mai zaman kan ta, ta na karkashin ikon kasar Turkiyya ne.

Ta ce kiran da su ka yi ya zama dole, domin iyaye su san irin halin da ‘ya’yan su kan shiga a wannan kasa, ta na mai cewa, babban abinda ke ci masu tuwo a kwarya shi ne, ko da wani abu ya samu wani ɗan Nijeriya babu inda zai kai kukan sa, saboda kasar ba ta nan ba ta can ne, kuma majalisar ɗinkin duniya ba ta san da ita ba.

Abike Dabiri-Erewa, ta ce duk abin da ya samu ɗan Najeriya sai dai su zuba ido, domin ba su da inda za su kai kukan su, shi ya sa gwamnati ke kira ga iyaye cewa abin da ya fi dacewa shi ne a daina tura yara kasar karatu.

Leave a Reply