Home Labarai Atiku Ya Bayyana Kaduwa Game Da Rasuwar Sarkin Funakaye

Atiku Ya Bayyana Kaduwa Game Da Rasuwar Sarkin Funakaye

379
0

Dan Takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya aike da ta’aziyya ga iyalai da al’ummar masarautar Funakaye da ke jihar Gombe, game da rasuwar Mai martaba Sarkin Funakaye Alhaji Muhammad Kwairanga.

A Cikin sakon ta’aziyyar da ya wallafa a shafin sa na Twitter, Atiku ya bayyana kaduwa da bikin ciki bisa rasuwar matashin basaraken a shekaru 43.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Abdulrasheed Shehu ya raba wa manema labarai, Atiku Abubakar ya ce rasuwar basaraken akwai radadi, amma sarkin ya bar tarihin da za a dade ana tunawa da shi.

A bani bangare kuma, Atiku Abubakar ya yi Allah-Wadai da kisan gillar da aka yi wa Shaikh Goni Aisami, wanda ake zargin wasu sojaji da aikatawa.

Yayin da ya ke mika ta’aziyya ga iyalan malamin, Atiku ya ce ‘kisan gillar da aka yi ma shi lamari ne da ke nuna yadda abubuwa su ka lalace a Nijeriya, ta yadda ran dan Adam ba ya da kima da martaba.

Leave a Reply