Home Home KOTUN Zaɓen Shugaban Ƙasa Ta Ɗau Zafi

KOTUN Zaɓen Shugaban Ƙasa Ta Ɗau Zafi

93
0
Kotun ƙoli da ke birnin London, ta ce ‘yan Nijeriyar da ke son shigar da ƙarar kamfanin man fetur na Birtaniya Shell sun makara.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bayyana aniyar gayyato ma’aikatan wucin-gadi na Hukumar Zaɓe ta Ƙasa domin su bada shaidar rashin sahihancin nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shekara ta 2023.

Atiku Abubakar, ya ce zai gabatar da su ne a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa da keAbuja.

Masu bada shaidar uku da za a gabatar a gaban alƙalan kotun, su na daga cikin ma’aikatan wucin-gadin zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Atiku Abubakar dai ya yi zargin an tafka gagarumin maguɗi, don haka ya shigar da ƙarar rashin amincewa da sakamakon zaɓen, inda ya nemi kotu ta ba shi nasara ko kuma ta soke zaɓen a sake wani sabo.

Yayin da ake sauraren ƙarar da Atiku ya shigar a ranar Laraba, an kira mai bada shaida na 11 da Atiku ya gabatar, amma da aka kira mai bada shaidar na uku, nan take lauyoyin Tinubu da APC da hukumar zabe su ka ce ba su yarda da wanda Atiku ke so ya bada shaidar ya yi magana a gaban alƙalan ba.

Leave a Reply