Home Home ‘Yan Sanda Sun Rufe Majalisar Jihar Nasarawa Saboda Rikicin Shugabanci

‘Yan Sanda Sun Rufe Majalisar Jihar Nasarawa Saboda Rikicin Shugabanci

1
0

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa, ta rufe Majalisar Dokoki ta jihar domin gudun rikici, bayan an samu ɓangarori biyu na ‘yan majalisar da ke adawa da juna.

A ranar Talatar da ta gabata, ɓangare ɗaya ya zaɓi Daniel Ogazi a matsayin kakakin Majalisar, yayin da ɗaya bangaren su ka zaɓi Ibrahim Balarabe.

Kakakin ‘yan sanda na jihar DSP Ramhan Nansel, ya ce Kwamashinan ‘Yan Sanda na jihar Maiyaki Baba ne ya bada umarnin rufe Majalisar bayan tattaunawa da sauran masana tsaro.

DSP Ramhan Nansel, ya ce ba za a bar kowane ɓangare ya shiga Majalisar ba har sai ƙura ta lafa.