Ƙungiyar dillancin man fetur ta Nijeriya DAPPMAN, ta yi alƙawarin samar da manyan motoci kirar Bas guda 100 domin tallafa wa yunƙurin gwamnati na cire tallafin man fetur.
Da take magana bayan ganawar su da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugabar ƙungiyar Dame Winifred Akpani, ta ce su na goyon bayan matakin gwamnati na cire tallafin 100 bisa 100.
Ta ce cire tallafin ba ya nufin tsawwala farashin sa ko kuma rage yawan sa a tsakanin ‘yan Najeriya, magana ce ta yin abin da ya dace game da tallafi a harkokin man fetur.
Tun farko dai gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya sun shirya shiga yajin aikin gama-gari, amma daga baya su ka janye bayan sun gana da shugaban ƙasa.