Kotun koli ta Nijeriya, ta tabbatar wa gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola kujerar sa ta gwamma.
Idan dai ba a manta ba, dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP Ademola Adeleke ne kotun sauraren kararrakin zabe ta ce ya lashe zaben jihar Osun a hukuncin farko, inda jam’iyyar APC ta garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.
A hukuncin da ta yanke a wancan lokacin, kotun ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke cewa akwai mishkiloli a ciki.
Karanta Labaru Masu Alaka: Sanata Adeleke Ya Cancanci Ya Rike Gwamnan Osun – Kotu
Adeleke ya garzaya kotun Koli domin bin hakkin sa, Sai dai kotun, wadda Alkalai bakwai su ka zauna, ta yanke hukuncin cewa kotun daukaka kara ta yi daidai wajen soke hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe.
Sai dai daga cikin Alkalai bakwai da su ka yi zaman sauraren shari’ar, biyu daga cikin su ba su amince da hukuncin ba.
You must log in to post a comment.