Home Labaru Buhari Ya Sake Nada Boss Mustapha Da Abba Kyari

Buhari Ya Sake Nada Boss Mustapha Da Abba Kyari

764
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da sake nada Mista Boss Mustapha a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, da kuma Abba Kyari a matsayin Shugaban ma’aikata na fadar Shugaban kasa.

Karanta Labaru Masu Alaka: Za A Bayyana Sunayen Ministoci A Watan Yuli – Boss Mustapha

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya fitar.

Garba Shehu, ya ce nadin mutanen biyun ya fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2019.

Idan dai za a iya tunawa, a baya wasu masu ruwa da tsaki sun gudanar da zanga-zangar neman shugaba Buhari ya cire Abba Kyari daga mukamin shugaban ma’aikata.

Leave a Reply