Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara, ta ce za ta yi sulhu tsakanin wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da ‘yan kungiyar tsaro na sa-kai da aka sani da ‘yan banga.
Hakan ya sa jami’an tsaron sa-kan su ka saki ‘yan bindiga 25 da ke tsare a hannun su domin wanzar da zaman lafiya a jihar Zamfara.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Mohammed Shehu, ya ce an saki ‘yan bindigar ne sakamakon sulhun da ‘yan sanda ke yi tsakanin ‘yan bindigar da ‘yan kungiyar sa-kai.
Karanta Labaru Masu Kama: ‘Yan Ta’adda Sun Mika Bindigogi 216
Rundunar ta ce, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Usman Nagogo, ya yi nasarar karbo mutane 25 da aka tsare tun ranar 9 ga watan Afrilu na shekara ta 2019 a masarautar Dansadau da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Yayin da ya ke karbar wadanda aka sako, Kwamishinan ‘yan sandan ya yaba wa kungiyar tsaron saboda cika alkawarri da su ka yi na sakin wadanda su ke tsare da su, tare da bukatar bangarorin biyu su zauna lafiya.