Home Labaru Kotun ECOWAS Ta Umarci Gwamnatin Nijar Ta Biya Iyalan Ba’Are Mainasara CFA...

Kotun ECOWAS Ta Umarci Gwamnatin Nijar Ta Biya Iyalan Ba’Are Mainasara CFA 7,564,250

25
0

Kotun ECOWAS ta umarci gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta biya CFA 7,564,250 ga iyalan tsohon shugaban kasar na mulkin soji, Janar Ibrahim Ba’are Mainasara, wanda aka yi wa kisan gilla.

Kotun ta kuma ba gwamnatin Jamhuriyar Nijar wa’adin mako biyu ta gabatar mata shaidar yunkurin fara biyan kudaden ga magadan Janar Bare Mainasara, wanda ya mulki kasar daga 1996 kafin a kifar da gwamantin sa a juyin mulkin da aka kashe shi a 1999.

Alkalan kotun mai zama a birnin Abidjan na kasar Kwaddabuwa sun yanke hukuncin biyan kudaden ne a matsayin diyyar abin da magadan marigayin suka kashe na kudaden shari’a.

Sanarwar da mai Magana da yawun kotun, Elohor Ovadje, ya fitar ta ce kudaden, kamar da lauyan iyalan Ba’are Mainasara, Chaibou Abdourahaman, ya bayyana sun hada da kudaden daukar lauyoyi da na tafiye-tafiye da na harajin VAT da sauran su.

Mai Shari’a Dupe Atoki, wanda ya karanta hukuncin kotun, ya ce alkalan kotun sun yanke hukuncin ne bayan karar da iyayalan Janar Ba’are Mainasara suka kara shigarwa a shekarar 2020.