Home Labaru Angela Merkel Ta Ja Hankalin Mata A Jamus

Angela Merkel Ta Ja Hankalin Mata A Jamus

14
0

Shugabar gwamnatin Jamus mai barin gado, Angela Merkel, ta nuna bukatar mata a Jamus su kara shiga cikin harkokin siyasa, musamman ma shiga a dama da su a harkokin jam’iyyu.

A wata hirar da ta yi da jaridar Sueddeutsche Zeitung, Angela Merkel, ta ce tsarin tafiyar zamanin yau na bukatar mata su rika gogayya da maza a harkar siyasa akasin yanda abin yake a baya.

A cewar ta muddin jam’iyyun siyasa na son tafiya da kowa, to lallai ne mata su kasance a matakan su na jagoranci gwargwadon yadda maza ke yi.

Shugabar gwamnati ta Jamus, wadda ta kasance mace ta farko da ta taba rike mukamin shugabancin gwamnati a kasar, ta kawo karshen takararta ne bayan mulkin shekaru 16 a jere.

Armin Laschet, wanda shi ne dan takarar jam’iyyar CDU ta Angela Merkel a zaben da ya gabata, ya bayyana aniyar sa ta jagorantar jam’iyyar kafin lokacin da zai yi adabo da siyasa.

Nan gaba ne dai jam’iyyar za ta sake zaben shugabannin ta.