Home Labaru Kotu Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Ga Matashin Da...

Kotu Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Ga Matashin Da Ya Kashe Mahaifin Sa

649
0
Zargin Kisa: Kotu Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Kan Matashin Da Ya Kashe Mahaifin Sa
Zargin Kisa: Kotu Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Kan Matashin Da Ya Kashe Mahaifin Sa

Wata kotu a a Ikeja ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani bakanike mai suna Rasak Abiona, da ya kashe mahaifin sa mai shekaru 62 ta hanyar buga masa da rodi a kai.

Wata majiya ta ce, alkalin kotun mai shari’a Oluwatoyin Taiwo ta zartar da hukuncin ne a lokacin zaman kotun na ranar Litinin ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Rasak ya kashe mahaifin sa ne sakamakon sabanin da su ka samu a kan wata kadara da ke jihar Legas, sai  dai mai shari’a Taiwo ta ce masu kara sun gabatar da isassun shaidun da su ka kore duk wani shakku da cewa matashin ne ya kashe mahaifin sa.

Taiwo ta kara da cewa, wanda ake zargi ya amsa laifin sa a cikin rahoton da ya rubuta a ofishin rundunar ‘yan sanda, haka kuma ya gaza kare kansa ko gabatar da wata kwakwarar hujja da za ta wanke shi daga zargin da ake yi masa.

Kotun ta ce, wanda aka gurfanar ya gaza gabatar da hujjar da za ta gamsar da kotu cewa, mahaifin sa ya mutu ne sakamakon faduwar da ya yi a kan karfen rodi, wanda hakan ya sa aka yankewa Rasak hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifin aikata kisan kai, laifin da ya sabawa sashe na 221 na kundin manyan laifuka a jihar Legas, da aka kirkira a shekara ta 2011.

Leave a Reply