Home Labaru Za A Gudanar Da Bincike A Kan Shugaban APC Na Jihar Neja

Za A Gudanar Da Bincike A Kan Shugaban APC Na Jihar Neja

499
0
APC Na Jihar Neja
Za A Gudanar Da Bincike A Kan Shugaban APC Na Jihar Neja

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta bukaci shugaban jam’iyyar APC na jihar Muhammad Jibril Imam ya gabatar da kan sa bisa zargin sa almundahanar wasu kudade.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ce ana zargin Jibril Imam da wawure kudin jam’iyyar tun da ya hau mulkin a shekara ta 2015.

Haka kuma kwamishinan ya ce an mika korafi a kan Muhammad Jibril Imam sakamakon zargin sa da wawure kudaden jam’iyyar tun daga kan kudaden fom da ‘yan takara suka siya.

Ya ce masu korafin sun zargi shugaban jam’iyyar da kashe kudaden tare da wasu dalilai ba.

Kwamishinan ya kara da cewa, wasu ‘yan majalisar zartarwar jam’iyyar jihar ne su ka mika korafin, inda su ke zargin shugaban da amfani da kujerar sa ta hanyar da bata dace ba.

A karshe ya ce, suna cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin, domin gano ko akwai gaskiya a cikin zargin masu korafin.