Home Labaru Kano: Babu Fita Ranakun Litinin, Talata, Alhamis Da Asabar — Ganduje

Kano: Babu Fita Ranakun Litinin, Talata, Alhamis Da Asabar — Ganduje

655
0
Kano: Babu Fita Ranakun Litinin, Talata, Alhamis Da Asabar — Ganduje
Kano: Babu Fita Ranakun Litinin, Talata, Alhamis Da Asabar — Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano, ta ce har yanzu dokar kulle ta na aiki a ranakun Litinin da Talata da Alhamis da kuma Asabar.

Kwamishinan yada labaran jihar Muhammad Garba ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce gwamnatin ta dauki wannan matakin ne domin biyaya ga umurnin gwamnatin tarayya na sassauta dokar kullen da aka saka domin dakile yaduwar cutar COVID-19 a Nijeriya.

Gwamnatin jihar ta kuma fitar da sabbin ka’idoji da kuma dokoki a kan yadda za a rika zuwa kasuwanni da sauran wuraren hada-hadar jama’a domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa, bayan tuntubar kwararru a bangaren lafiya da kuma bita kan halin da ake ciki a jihar, an bada umarnin zirga-zirga da bude wuraren bauta a ranakun Lahadi da Laraba da kuma Juma’a daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.

Sai dai Sanarwar ta ce, duk da sassaucin da aka yi, dokar hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi ta na nan har yanzu, sai dai masu jigilar kayan abinci da na amfanin yau da kullum.