Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da buƙatar da tsohon shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar ‘yan sandan Nijeriya Abba Kyari ya gabatar a gaban ta, ya na neman kotun ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi ma shi.
Yayin zaman kotun, mai shari’a Emeka Nwite ya yi watsi da buƙatar Abba Kyari, ya na mai cewa kotun ta na da hurumin sauraren ƙararrakin da ke da alaƙa da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi, kamar yadda kundin tsarin mulki da dokar da ta kafa hukumar NDLEA su ka ba ta dama.
Abba Kyari ya shaida wa kotun cewa, hukumar NDLEA ta yi gaugawar gabatar da shi a gaban kotu tun kafin a kammala bincike, ya na mai cewa kamata ya yi hukumar ta ba ‘yan sanda damar gudanar da bincike a cikin gida kafin ta ɗauki mataki.
Ya ce ‘yan sanda sun gudanar da bincike a kan lamarin, kuma har sun gabatar da rahoton cikin gida ga rundunar ‘yan sanda.
Abba Kyari, ya ce dokar aikin ‘yan sanda ta ce, hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta na da ikon da za ta gudanar da bincike tare da ladabtar da jami’an ‘yan sanda, kamar yadda majalisar ƙoli ta ayyukan shari’a ke da ikon ladabtar da ma’aikatan shari’a, sai dai alƙalin kotun ya ce, ikon da hukumar kula da ayyukan ‘yan sandan ke da shi bai zarta ikon da kotun tarayya ke da shi ba.
You must log in to post a comment.