Home Labarai Kotu Ta Yi Fatali Da Ƙarar Da Abba Kyari Ya Shigar a...

Kotu Ta Yi Fatali Da Ƙarar Da Abba Kyari Ya Shigar a Kan NDLEA

111
0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta kori ƙarar da dakataccen
Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda DCP Abba Kyari ya
shigar a kan Hukumar NDLEA.

Abba Kyari dai ya maka hukumar NDLEA kotu, ya na neman ta
biya shi diyyar naira miliyan 500 na tauye ma shi ‘yanci da ta yi.

Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya kori ƙarar ne bisa dalilan rashin
gabatar da ƙwararan hujjoji daga ɓangaren lauyoyin Abba Kyari.

Alkalin kotun, ya nuna su kan su lauyoyin Abba Kyari ba su
ɗauki ƙarar da ya shigar da muhimmanci ba.