Home Labaru Biafra: Kotu Ta Yi Watsi Da Laifuka 8 Cikin 15 Da Ake...

Biafra: Kotu Ta Yi Watsi Da Laifuka 8 Cikin 15 Da Ake Tuhumar Nnamdi Kanu Da Su

53
0

Wata Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da
laifuffuka takwas daga cikin goma sha biyar da gwamnatin
tarayya ke tuhumar Nnamdi Kanu da su.

Gwamnatin tarayya dai ta dauko Nnamdi Kanu daga kasar
Kenya, inda ta maka shi kotu bisa zargin aikata ayyukan
ta’addanci.

A zaman kotun na ranar Juma’ar nan, Alkalin kotun Binta
Nyako ta yi fatali da laifuffuka takwas da gwamnati ke zargin
Nnamdi Kanu ya aikata, saboda babu hujjar da ke nuna cewa
wanda ake zargin ya aikata.

Amma ta ce akwai alamun gaskiya a cikin wasu laifuffukan, don
haka za a cigaba da gurfanar da Nnamdu Kanu domin ci-gaba da
sauraren karar.

Kotun, ta ce dauko shi da aka yi daga wata kasa ya halasta,
domin tuni an alamta neman sa ruwa a jallo.