Home Labaru Kotu Ta Yanke Wa Mutum Uku Hukuncin Kisa Kan Satar Waya Da...

Kotu Ta Yanke Wa Mutum Uku Hukuncin Kisa Kan Satar Waya Da Kwamfuta A Ekiti

98
0

Wata Babbar Kotu da ke Ekiti, ta yanke ma wasu mutane uku
hukunci kisa ta hanyar rataya bisa samun su da laifuffukan
fashi da makami.

An dai gurfanar da masu laifin ne gaban kotu tun a watan Janairun shekara ta 2020, bisa laifuffuka hudu da su ka haɗa da fashi da makami.

Mai shari’a Bamidele Omotoso, ya ce abubuwan da su ka aikata sun hada da sace wayoyin mutane da kwamfuta da takalma da cajojin waya, wadanda aka kiyasta kudin su ya kai naira dubu 186.

Kotun ta ce mutanen uku sun yi amfani da makamn da su ka hada adda da katako wajen kai hari da satar kayan.

Wata sanarwa da ‘yan sanda su ka fitar, ta ambato ɗaya daga cikin shaidu na cewa, su na cikin barci matasan su ka afka gidan su tare da kwashe masu kayayyaki da kuma yi masu barazana da makaman da su ke dauke da su.

Leave a Reply