Home Labaru Kiwon Lafiya Ana Wata Ga Wata: Kungiyar Likitocin Najeriya Za Su Fara Yajin Aiki...

Ana Wata Ga Wata: Kungiyar Likitocin Najeriya Za Su Fara Yajin Aiki Ranar Laraba

1
0

Kungiyar likitoci ta Nijeriya NARD, ta ce za ta fara yajin
aikin kwanaki biyar idan har gwamnati ba ta biya bukatun ta
ba.

Shugaban kungiyar Emeka Innocent ya sanar da haka, inda ya ce kungiyar ta dauki marakin ne a zaman da ta yi ranar Litinin da ta gabata.

Kungiyar ta ce za ta fara yajin aikin ne da misalin karfe 8 na safiyar Laraba 17 zuwa ranar Litinin 22 ga watan Mayu na shekara ta 2023.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 29 ga watan Afrilu ne kungiyar ta sanar da cewa za ta fara yajin aikin makonni biyu idan har gwamnati ba ta biya bukatun ta ba.