Home Labaru Obasanjo Ya Dukufa Sasanta Rikicin Tigray

Obasanjo Ya Dukufa Sasanta Rikicin Tigray

31
0

Babban jami’in jin-ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya Martin Griffiths, da jakadan musamman na Tarayyar Afrika Olusegun Obasanjo, sun kai ziyara yankin arewacin Tigray na kasar Habasha, domin tattaunawa a kan batun isar da kayan jin-ƙai da yiyuwar tsagaita wuta a rikicin da aka shafe shekara ana gwabzawa.

Rahotanni sun ce Mista Griffiths da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, tuni sun isa birin Mekelle a lokaci guda.

Kafar talabijin ta yankin Tigray ta ruwaito cewa, mutanen biyu sun gana da shugaban gwamnatin Tigray Dr Debretsion Gebremichael a ofishin sa, a kan rikicin su da Habasha da kuma yadda za a isar da kayan jin-ƙai da wasu batutuwa da su ka shafi yankin.

Ta ce daga baya Obasanjo da Mista Griffiths sun koma Addis Ababa babban birnin Habasha.