Home Labaru Kotu Ta Yanke Wa Evans Hukuncin Daurin Rai Da Rai

Kotu Ta Yanke Wa Evans Hukuncin Daurin Rai Da Rai

84
0

Wata kotu da ke zaman a Ikeja na jihar Legas, ta yanke wa kasurgumin mai garkuwa da mutane Chukwudimeme da aka fi sani da Evans hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.

An dai yanke wa Evans da abokan huldan sa biyu da su ka hada da Uche Amadi da Okwuchukwu hukunci ne bayan an kama su da laifin garkuwa da mutane.

Mai shari’a Hakeem Oshodi da ya yanke hukunci, ya ce an kama mutanen da laifi ne bayan hujjoji sun nuna cewa lallai sun aikata laifuffukan da ake zargin su da aikatawa.