Home Labaru Kotu Ta Ba Ganduje Da APC Nasara A Zaben Gwamnan Jihar Kano

Kotu Ta Ba Ganduje Da APC Nasara A Zaben Gwamnan Jihar Kano

457
0

Shari’ar da ake yi tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP mai adawa ta zo karshe a kotun farko da ke sauraron korafin zaben bayan da Alkali ta yi watsi da karar da PDP ta shigar.

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kano, ta tabbatar da nasarar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar.

Shugabar Alkalan da ke sauraren karar Mai shari’a Halima Shamaki, ta yi fatali da korafin da jam’iyyar PDP ta gabatar a zaman karshen da ta yi a ranar Larabar nan.

Daya daga cikin Hadiman gwamna Ganduje Salihu Tanko Yakassai ya tabbatar da hakan, inda ya fito a shafin sa na Tuwita ya na taya Maigidan sa murnar nasarar da ya samu.

Tuni dai jami’an tsaro sun cika jihar Kano domin kwantar da tarzoma idan ta tashi.