Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja, ta ki tsawaita
wa’adin wucin-gadin da ta bada na dakatar da Hukumar Zabe
ta Kasa da shugaban ‘yan sandan Nijeriya da Babban Lauyan
Tarayya daga gurfanar da dakataccen kwamishinan zabe na
jihar Adamawa Hudu Yunusa Ari.
Hukumar zabe dai ta na neman a gurfanar Hudu Yunusa Ari saboda ayyana Sanata Binani da ya yi a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa a ranar 15 ga watan Afrilu, yayin da ake ci-gaba da kidayar kuri’u.
Kotun, ta umarci bangarorin da ke da hannu a lamarin, wadanda su ka hada da hukumar zabe da shugaban ‘yan sanda da babban lauyan tarayya a matsayin wadanda ake tuhuma su
cigaba da kasancewa a halin da ake ciki har sai an yanke hukunci mai inganci.
Haka kuma, Kotun ta bukaci wadanda ake kara su gurfana a gaban ta ranar 18 ga watan Yuli, domin nuna dalilin da ya sa ba za a hana su gurfanar da kwamishinan zaben da aka dakatar ba.