Home Labaru Gwamnatin Najeriya Za Ta Sake Duba Batun Albashin Ma’aikata – Akpabio

Gwamnatin Najeriya Za Ta Sake Duba Batun Albashin Ma’aikata – Akpabio

102
0

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya tabbatar
wa ma’aikatan Nijeriya cewa gwamnati a shirye ta ke domin
sake duba albashin su, a wani mataki na rage masu raɗaɗin
cire tallafin man fetur.

Sanatan ya bayyana haka ne, lokacin da ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Ekiti Abiodun Oyebanji da ‘yan majalisar wakilai na jihar.

Ya ce gwamnatin shugaba Tinubu ta cire tallafin man fetur ne domin magance matsalar cin hanci da rashawa a ɓangaren man fetur, lamarin da ya ce zai sa gwamnati ta fara yaki da rashawa gadan-gadan.

Godswill Akpabio, ya ce idan da ba a cire tallafin man fetur ba, Nijeriya ba za ta iya tafiyar da harkokin ta yadda ya kamata ba a cikin shekaru masu zuwa.

Leave a Reply