Jam’iyyar APC, ta ce shugaba Tinubu ba ya bukatar kamun-
kafa a shari’ar da ake kalubalantar nasarar sa a zaben da ya
gabata.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Twitter, APC ta ce zargin da wani Mista Jackson Ude ya yi cewa Shugaba Tinubu ya yi magana ta waya da shugaban Alkalan Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a kan batun ba gaskiya ba ne.
Sanarwar, wadda Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar APC Felix Morka ya fitar, ya ce Mista Ude ya kirkiri karya ne a kan wannan batu da ke gaban Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa.
Ya ce ko shakka babu, Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC sun lashe zaben shugaban kasa kuma ba ya bukatar kamun-kafa wajen shugaban Alkalan Nijeriya dangane da shari’ar.
Felix Morka, ya ce ‘yan Nijeriya su na da basira kuma za su yi watsi da wadannan kalamai marasa tushe na ‘yan adawa da sojojin haya.