Home Labaru Hukumar NDLEA Ta Kama Hodar Ibilis Ta Biliyan N2 A Abuja

Hukumar NDLEA Ta Kama Hodar Ibilis Ta Biliyan N2 A Abuja

129
0

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) kama wani ɗan Nijeriya mazauni ƙasar Liberia Maduabuchi Chinedu, ɗauke da hodar ibilis mai nauyin kilo giram 9.3 wanda darajarta ta kai Naira biliyan 2.7 a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke nan Abuja.

Wanda ake zargin wanda ɗan asalin jihar Imo, yana zama a ƙasar Liberia ne a matsayin mai haƙar ma’adinai.

Mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi, yace sun kama wanda ake zargin ne sakamakon binciken haɗin gwiwa da jirgin ƙasar Ethiopia 911 a filin jirgin sama na Abuja a ranar Larabar da ta gabata inda aka gano hodar a cikin kayansa.

Jami’in ya ce yayin biciken farko, Chinedu ya yi iƙirarin cewa ya bar Nijeriya zuwa Liberia ne a 2018 inda a yanzu ya sami izinin zaman ƙasar.

Ya ci gaba da cewa Chinedu ya faɗa musu matsin rayuwa da buƙatar kuɗi don kula da lafiyar mahaifiyarsa ce ya sanya shi neman taimako a wajen wani abokinsa wanda ke zaune Addis Ababa wanda shi ne ya ba shi aikin safarar hodar zuwa Abuja a kan kuɗi Naira miliyan 1.

Babafemi ya ce da farko an shirya Chinedu ya kai hodar Ivory Coast ne amma daga bisani aka canza tsarin zuwa Nijeriya.

Leave a Reply