Home Labarai Shettima Yafi Cancantar Mara Min Baya – Bola Tinubu

Shettima Yafi Cancantar Mara Min Baya – Bola Tinubu

66
0

Dan Takarar shugaban kasa n a Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda ya fi cancantar zama mataimakin sa a zaben shekara ta 2023.

Tinubu ya shaida wa taron gabatar da wanda zai mara masa baya cewa rayuwar siyasar Sanata Shettima ta bayyana shi a matsayin wanda ya cika dukkan maradun da ake bukata wajen ganin Jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben shekara ta 2023.

Ya ce ya kammala duk shirin da ya kamata, kuma yana farin ciki da zabin abokin sa kuma dan’uwa Sanata Shettima a matsayin abokin takara.

Bola Tinubu, ya ce ya karanta rubuce-rubuce da korafe-korafen da jama’a ke yi a kan zabin Shettima, kuma a matsayin shi na mai bin tafarkin dimokiradiya da neman ci-gaba, ya fahimci matsayin da wasu jama’a ke gabatarwa kuma yana mutunta su, amma ya na da yakinin cewa bai yi kuskure wajen zaben Kashin Shettima ba.

Ya ce yana nan a akan manufofin da aka kafa jam’iyyar APC da banbancin da ke tsakanin jama’ar kasa, don haka su na bukatar nasara domin sama wa Nijeriya ci-gaban da ake bukata.