Home Labaru Kotu Ta Cigaba Da Tsare Sowore

Kotu Ta Cigaba Da Tsare Sowore

196
0
Za Mu Girmama Kotu A Kan Sowore - Malami
Za Mu Girmama Kotu A Kan Sowore - Malami

Alkalin wata babbar kotu da ke Abuja Nkeonye Maya, ya yi watsi da karar da babban lauya Femi Falana ya shigar ya na kalubalantar tsare Yele Sowore da hukumar tsaro ta SSS ke yi.

Idan dai ba a manta ba, jami’an tsaro sun kama Sowore bisa kokarin shirya zanga-zanga a fadin Nijeriya, domin nuna gazawar gwamnati wajen samar da tsaro da ababen more rayuwa.

Kakakin runndunar Peter Afunanya, ya ce hukumar ta gano cewa, Sowore ya na tattaunawa da wasu mutane a wasu kasashen waje a kan wannan gangami, lamarin da ya sa dole a taka ma shi burki don kada ya kawo rudani a Nijeriya.

Bisa hukuncin da alkali Nkeonye Maya ya yanke, Sowore zai cigaba da kasancewa a tsare har sai wa’adin kwanakin da kotu ta dibar ma shi ya cika.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/libertytvnews

Twitter: https://twitter.com/libertytvnews

Instagram: https://instagram.com/libertytvng

Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??

zeno.fm/libertyradioabuja

Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?

Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.

Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com