Home Labaru ‘Yan Nijeriya Da Saudiyya Ta Yanke Wa Hukuncin Kisa

‘Yan Nijeriya Da Saudiyya Ta Yanke Wa Hukuncin Kisa

925
0

Gwamnatin tarayya, ta ce ‘yan Nijeriya 23 da aka yanke wa hukunci a kan safarar miyagun kwayoyi a kasar Saudiyya su na nan da ran su.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kakakin ma’aikatar fursunoni na harkokin waje Ferdinand Nwonye, ya ce har yanzu gwamnati na tattaunawa da su.

Ya ce an ja hankalin ma’aikatar harkokin waje a kan rahotannin kafofin watsa labarai cewa, an yanke wa ‘yan Nijeriya 23 hukuncin kisa bisa laifin da ya shafi miyagun kwayoyi a kasar Saudiyya.

Ferdinand ya kara da cewa, ma’aikatar na kan tattaunawa da hukumar Nijeriya a kasar Saudiyya, kuma ta tabbatar da cewa labarin karya ne don haka a yi watsi da shi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/libertytvnews

Twitter: https://twitter.com/libertytvnews

Instagram: https://instagram.com/libertytvng

Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??

zeno.fm/libertyradioabuja

Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?

Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.

Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com