Home Labaru Jihar Sokoto: Ana Farautar ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Dan Majalisa

Jihar Sokoto: Ana Farautar ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Dan Majalisa

289
0

Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto na fararutar wasu ‘yan bindiga da suka sace daya daga cikin dan  majalisar dokokin Jihar mai wakiltar mazabar Denge Shuni, Aminu Magaji Bodai.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘ASP Muhammad Sadiq Abubakar, ya tabbatar da sace dan majalisar, inda ya ce sun sami bayanan da ke cewa, wasu ‘yan bindiga da yawansu ya kai 10, sun kutsa cikin kauyen Bodai dake Karamar Hukumar Denge Shuni suka sace dan majalisar.

ASP Muhammad ya ce, ‘yan sandan na gudanar da farautarsu a dazuka da zummar ceto dan majalisar tare kuma da cafke ‘yan bindigar.

Garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa na ci gaba da addabar wasu jihohin arewacin Najeriya, koda yake, jami’an tsaro na aiki tukuru domin ganin sun kawo karshen mataslar.