Home Labaru Babu Abin Da Ke Tsakani Na Da Buhari Face Biyayya Sau Da...

Babu Abin Da Ke Tsakani Na Da Buhari Face Biyayya Sau Da Kafa – Osinbajo

266
0

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi watsi da rade-radin da ke yawo game zargin cewa ana zaman doya da manja tsakanin sa da shugaba Muhammadu Buhari, lamarin da ya ce kanzon kurege ne da shaci fadi da ke kai komo musamman a shafukan sada zumunta.

Farfesa Osinbajo, ya ce babu abin da ke tsakanin sa da shugaba Buhari face biyayya sau da kafa da kuma yi wa juna kyakkyawar fata.

A cikin sakon sa na murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan Nijeriya, Osinbajo ya jaddada goyon baya tare da biyayya sau da kafa ga shugaba Muhammadu Buhari.

Mataimakin shugaban kasar ya sake jaddada cewa, shugaba  Buhari sai sauke nauyin dukkan alkawurran da ya dauka, inda ya misalta shi a matsayin managarcin ubangida mafi soyuwa da ya taba aiki a karkashin sa.