Home Labaru Babakere: EFCC Ta Kwakulo Motocin Alfarma 21 A Gidan Yari

Babakere: EFCC Ta Kwakulo Motocin Alfarma 21 A Gidan Yari

613
0
EFCC
EFCC

Jami’an hukumar hana zambar kudi da karya tattalin arziki EFCC sun kai wani samame gidan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, kan binciken da hukumar ke yi wa gwamnatin sa da ta shude.

Karanta Wannan: Belin El-Zakzakky: Hukumar DSS Ta Amince Da Umurnin Kotu

Jami’an hukumar ta EFCC, sun kuma binciki gidan kanin sa Jafaru, da kuma na abokin sa Sha’aya Mafara.

Motoci na alfarma guda 21 ne jami’an hukumar ta EFCC su ka samu a cikin gidan na Yari, wanda shi ne tsohon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.

Hukumar ta ce binciken da za a yi wa Yari, shi ne zai tabbatar da ko ta yaya ya tara wadannan motocin.

Tsohon gwamnan jihar Zamfaran yana fuskantar bincike ne kan zargin da ake masa na karkatar da wasu kudade naira bilyan 19 wadanda suka fito daga asusun nan na Faris Klub, da naira bilyan 35 da ya ce ya kashe a kan hidimar ‘yan gudun hijira, da hana zaizayar kasa, da kuma ta yanda ya tarawa Jihar bashin dimbin kudi.

Tun a shekarar 2017 ne hukumar ta EFCC take bibiyan gwamnan sai dai garkuwar da yake da ita a matsayin sa gwamna ya sa ta kasa yi masa komai.