Home Home Kotu Ce Za Ta Raba Ni Da INEC – Obi

Kotu Ce Za Ta Raba Ni Da INEC – Obi

22
0
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Peter Obi, ya ce shi ne ya ci zaɓen da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu, don haka zai bi duk wani matakin shari’a domin ya ƙwato nasarar sa.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Peter Obi, ya ce shi ne ya ci zaɓen da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu, don haka zai bi duk wani matakin shari’a domin ya ƙwato nasarar sa.

Peter Obi, ya ce wannan ne karo na farko da ya fito duniya ya ke magana tun bayan kada kuri’ar da ya yi a zaɓen, don haka ya ce duk wani sako ko magana da aka danganta da shi a baya ba shi ya fada ba.

Dan takarar ya cigaba da cewa, sun ci zaɓen kuma za su tabbatar wa ‘yan Nijeriya haka.