Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya ce zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamitin sulhu bayan ya lashe zaben shekara ta 2023.
Rotimi Akeredolu, ya ce kwamitin zai zauna ne da sauran ‘yan takarar da su ka fafata da Tinubu domin yin sulhu da su.
Ya ce kwamitin zai hada da manya kuma dattawan jam’iyyar APC kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Gwamna Rotimi ya bayyana haka ne a Abuja, lokacin da hukumar zabe ta ba Tinubu shahadar lashe zaben shekara ta 2023.
You must log in to post a comment.