Ranar Litinin 8 ga watan Yuli, ake sa ran kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta cigaba da shari’a a kan bukatar Atiku Abubakar ta soke nasarar lashe zaben da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.
Tuni dai Atiku Abubakar ya gabatar da shaidu dubu 26 da 175 na takardun da ke tabbatar da zargin cewa ta hanyar magudi jam’iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa.
Karanta Labarun Masu Alaka: Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Atiku, PDP
Daga cikin shaidun kuwa, akwai takardun sakamakon kuri’un da aka kada yayin zaben daga jihohi takwas da su ka hada Jigawa, da Borno, da Gombe, da Bauchi, da Katsina, da Kebbi da Kaduna da kuma Kano.
Sai dai lauyoyin wadanda ake kara sun bukaci a yin watsi da haidun da Atiku Abubakar ya gabatar.Lauyan Atiku Abubakar Livy Uzoukwu ya shaida wa kotun cewa, sun shirya don soma kiran shaidun su don yiwa kotun karin bayani a kan takardun da su ka gabatar.