Home Labaru Gwamnatin Trump Ta Bankaura Ce Kawai – Birtaniya

Gwamnatin Trump Ta Bankaura Ce Kawai – Birtaniya

386
0
Donal Trump, Shugaba Kasar Amurka
Donal Trump, Shugaba Kasar Amurka

Jakadan kasar Birtaniya a Amurka ya caccaki gwamnatin Shugaba Trump, inda ya bayyana ta a matsayin bankaura kuma cike da rauni.

A cikin wata wasikar sirri da ta bayyana, Jakada Sir Kim Darroch, ya ce fadar gwamnatin Amurka karkashin shugabancin Donald Trump ta sukurkuce tare da rarrabuwa.

Sir Kim Darroch, Jakadan Kasar Birtaniya A Amurka
Sir Kim Darroch, Jakadan Kasar Birtaniya A Amurka

Sai dai duk da hakan, Mista Darroch ya yi gargadin cewa kada a yi watsi da shugaban Amurka, duk da yadda ya ke a halin yanzu.

Ma’aikatar harkokin waje ta Birtaniya ta ce, satar bayyana takardar da ke dauke da maganganun da aka yi ga jaridar Mail, an yi hakan ne da mummunar niyya, kuma ba ta musanta kalaman ba.

A cikin takardar, Sir Kim ya ce ba su ganin wannan gwamnatin za ta daidaita, domin sukurkutacciya ce ba ta da kan kado sannan ba ta yin abu a kan tsari.’

Karanta Labarun Masu Alaka: Trump Ya Fasa Kai Hari Iran

Sai dai a nashi bangaren, Donald Trump ya ce gwamnatin sa za ta cigaba da kasancewa mai nuna bambanci tare da fifita kasar Amurka a kan komai.