Home Labaru An Yi Wa Sojoji Kwanton-Bauna A Garin Damboa

An Yi Wa Sojoji Kwanton-Bauna A Garin Damboa

1362
0

Mayakan kungiyar Boko Haram, sun kai wa dakarun soji harin kwanton-bauna tare da kashe a Kalla biyar da kuma raunata wasu da dama kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Wata majiya ta ce adadin sojojin da su ka mutu zai iya karuwa saboda har yanzu ba a ga wasun su ba, bayan harin da mayakan su ka kai masu ranar Alhamis da ta gabata a garin Damboa na jihar Borno.

Karanta Labarun Masu Alaka: Boko Haram Ta Hallaka Mutane 20 A Iyakar Nijeriya Da Nijar

A cewar majiyar, dakarun sojin sun je yankin ne domin ci-gaba da sharar sansanin ‘yan Boko Haram, amma sai aka kai masu harin kwanton-bauna a hanyar su.

Karanta Labarun Masu Alaka: ‘Yan Boko Haram Sun Fara Hada Kai Da ‘Yan Bindiga A Zamfara

Kwamandan rundunonin dakarun soji da ke jihar Borno bigediya janar Bulama Biu, ya tabbatar da artabun da aka yi tsakanin sojoji da ‘yan ta’dda, amma ya ce rundunar soji ba ta rasa mutum ko daya ba.

Leave a Reply