Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce mutum takwas ne suka rasu ranar Lahadi washegarin Ranar Kirsimeti sakamakon kamuwa da cutar korona.
NCDC tace wasu mutum 1,547 kuma sun kamu da cutar a Lahadin, abin da ya sa jumillar adadin wadanda suka kamu ya kai 237,561, yayin da waɗanda cutar ta kashe kuma suka zama 3022.
Alƙaluman da NCDC ta fitar a ranar Asabar kuma sun nuna cewa mutum 20 ne suka mutu a ranar ta Kirsimeti.
Waɗanda suka kamun sun fito ne daga jiha 10, ciki har da Abuja babban birnin tarayya Abuja inda aka samu Karin mutum (806) Legas (401) Borno (166) Oyo (78) Ogun (47) Osun (30) Ekiti (7) Katsina (7) Kano (4) Jigawa (1).
You must log in to post a comment.