Home Home Mafarauta Sun Cafke ‘Yan Fashin Daji A Kaduna

Mafarauta Sun Cafke ‘Yan Fashin Daji A Kaduna

151
0

Wasu mafarauta a garin Udawa da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna sun kama wani dan bindiga a wani daji da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Mafarautan sun kuma kubutar da wasu mutanen kauyen su 9 da aka yi garkuwa da su a farmakin da suka kai wa ‘yan bindigar da ke addabar yankin.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa mafarautan sun yi wa barayin kwanton bauna ne kwanaki bayan da suka far wa ayarin motocin matafiya a kan babbar hanyar.

Wani mai fada a ji a yankin Muhammad Umaru ya ce dukkan wadanda aka ceto daga kauyen Udawa suke.

Leave a Reply