Home Labaru Buhari Zai Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Kan Makamashi

Buhari Zai Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Kan Makamashi

66
0

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken zai kawo ziyara Najeriya da Kenya daga 15 zuwa 20 ga watan Nuwamba.

Ofishin Harkokin Wajen Amurka ya ce Mista Blinken zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari ne, inda za su tattauna kan makamashi da harkokin lafiya da dimokuraɗiyya.

Kazalika idan ya je Kenya, Blinken zai tattauna da Shugaba Uhuru Kenyatta game da annobar korona da kuma matsalolin tsaro a maƙotanta kamar Ethiophia da Sumaliya da Sudan.

Wata sanarwa in ji ofishin ta bayyana cewa a Dakar babban birnin Senegal, Shugaba Macky Sall, zai jaddada ƙawancen ƙasashen biyu ne.