Home Labaru Kiwon Lafiya Korona: Ƙarin Mutum 547 Sun Kamu A Najeriya Ranar Asabar

Korona: Ƙarin Mutum 547 Sun Kamu A Najeriya Ranar Asabar

164
0
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 547 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Asabar.

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 547 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Asabar.

Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu da cutar a jihar Legas suke inda aka samu ƙarin mutum 110 da suka kamu da cutar a jihar yayin da jihar Oyo aka samu mutum 72 da suka kamu da cutar sai kuma Ribas mutum 56.

Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranar Asabar, Legas-110, Oyo-72, Ribas-56, Anambra-50, Osun-49, Delta-48, Abuja (Babban Birnin Najeriya)-42, Ekiti-29, Akwa Ibom-26, Abia-19, Kano-16, Edo-10, Benue-7, Ogun-6, Kaduna-5, Bayelsa-2

A jimillance, adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 198,786 sai dai 185,075 sun warke.

Akwai kuma mutum 2,590 da suka mutu.