Home Labaru Tsaro Mulkin Taliban: Mata A Afghanistan Sun Nuna Goyon Bayan Su

Mulkin Taliban: Mata A Afghanistan Sun Nuna Goyon Bayan Su

96
0
Wasu mata ƴan Afghanistan sanye da niƙabi sun zauna a sahun gaba a aji a wata jami'a a Kabul ranar Asabar, don nuna goyon bayansu ga dokokin Taliban masu tsauri kan raba mata da maza a wurin karatu.

Wasu mata ƴan Afghanistan sanye da niƙabi sun zauna a sahun gaba a aji a wata jami’a a Kabul ranar Asabar, don nuna goyon bayansu ga dokokin Taliban masu tsauri kan raba mata da maza a wurin karatu.

Kusan matan 300- rufe ruf tun daga sama har ƙasa kamar yadda sabuwar dokar sanya tufafi ta tanada- sun ɗaga tutotin Taliban a lokacin da wasu ke jawabin nuna kin jinin Yamma tare da nuna goyon bayansu ga dokokin Musulunci.

Wasu daga cikinsu sun sa shuɗin burqa, mai ɗan raga-raga a wurin idanu, amma mafi yawansu sun sa niƙabi ne mai rufe duka fuskan ban da idanu.

Da yawa daga cikinsu kuma sun sa safar hannu baƙa.